1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar IMF za ta tsame hannu daga shirin ceto Girka

Gazali Abdou TasawaJuly 30, 2015

Hukumar ta IMF ta ce za ta dauki wannan mataki idan har kasar ta Girka ba ta aiwatar da matakan tsuke bakin aljihun da aka gindaya mata ba ,idan kuma kasashen Turai ba su rage nauyin bashin da suke bin kasar ba

USA Christine Lagarde IWF Online-PK
Hoto: picture-alliance/dpa/IMF/S. Jaffe

Hukumar bada lamuni ta duniya ta IMF ta ce ba za ta shiga cikin shirin tallafa wa kasar Girka domin ceto ta daga matsalar bashinta ba matsawar Girkan da kanta ba ta amince ta aiwatar da illahirin matakan tsuke bakin aljihun da aka gindaya mata ba, matsawar kuma kasashen Turai ba su cimma matsaya daya ba ga rage bashin da suke bin kasar ta Girka.

Wani daga cikin shugabannin hukumar ta IMF ne ya bayyana hakan a wannan Alhamis inda ya ce sai idan wadannan sharudda biyu sun cika ne kadai hukumar za ta ba da hadin kanta ga shirin ceto kasar ta Girka.

A share daya kuma firaministan kasar ta Girka ne Alexis Tsipras ya yi barazanar sake shirya wani zaben raba gardama a ranar Lahadi mai zuwa kan batun, matsawar shirin nasa zai ci gaba da fuskantar tarnaki daga jam'iyyarsa da ke ci gaba da nuna adawarsu da matakin tsuke bakin aljihun da gwamnatin kasar ta amince da shi.