1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Coronavirus barazana ce ga rayuwar dan adam

Ramatu Garba Baba
January 27, 2020

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ta yi kuskure a yayin baiyana sakamakon bincikenta kan annobar Coronavirus da yanzu haka ke ci gaba da bazuwa a wasu sassan duniya.

China Temperaturmessung in Wuhan
Hoto: Getty Images/AFP/H. Retamal

Sabon binciken da ta ce ta yi, ya nunar da munin lamarin fiye da yadda ake zato inji mai magana da yawun hukumar. Tuni sanarwar ta soma shan suka a sakamakon sakaci da ake zargin hukumar da yi na kin daukar matakin gaggawa a yayin barkewar annobar.


A karon farko dai, cutar ta kashe mutum guda a Beijing babban birnin Chainan, an gano marigayin ya dawo ne daga garin Wuhan inda Coronavirus ke ta tafka ta'adi. Annoba ce da ka iya yaduwa kamar wutar daji inji masana kimiya inda tuni aka soma yin kira ga hukumar lafiya ta shawo kanta.