1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Sake bullar kwayar cutar Ebola a Guinea

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 14, 2023

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cewa za ta gudanar da taron gaggawa, bayan da aka sake samun bullar kwayar cutar Ebola a kasar Guinea.

Guinea | Ebola | WHO
Sake bullar Ebola a Guinea, ya haifar da fargabaHoto: Luke Dray/Getty Images

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa, za ta gudanar da taron gaggawar ne domin tattauna batun allurar riga-kafin kwayar cutar ta Ebola MARVAC. Wadanda ke kokarin hada riga-kafin ta MARVAC sun hadar da masu bincike kan allurar riga-kafi da masu samar da ita, wadanda aka dorawa alhakin samar da riga-kafin cutar mai kisan farat-daya. A baya dai kwayar cutar Ebola ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama nahiyar Afirka, musamman a kasashen Guinea da Laberiya.