Hukumar OIM ta sanar da nutsewar mutane cikin teku
September 15, 2014Talla
Hukumar ta OIM ta sanar cewa, wasu 'yan kasar Falasdinu guda biyu da aka samu cetowa, sun tabbatar da wannan adadi, inda suka ce masu yi musu jagora ne suka haddasa wannan hadarin da gangan domin hallakar da su.
Tuni dai humomin kasar Italiya suka soma bincike kan wannan lamari, wanda idan har zargin ya zamana gaskiya, zai kasance nutsewar jirgin da tafi ko wace muni a 'yan shekarun bayan nan, ganin cewa ba hadari ba ne da ya zo daga Indallahi. Mutanen dai sun hada da Misrawa, da Falasdinawa, da 'yan Siriya da kuma 'yan kasar Sudan. Su ma daga nasu bangare, hukumomin kasar Libiya, sun sanar da nutsewar wasu mutane 'yan gudun hijira akalla 200 'yan asalin Afirka a ranar Lahadi a gabacin Tripoli.