Hukumar Tarayyar Turai ta ja hankalin Macron
May 8, 2017Talla
A cewar Mr. Jean Claude Juncker ba kananan kudade ne ake barnatarwa ga banza ba a Faransa a yanzu.
A nata bangaren gwamnatin Jamus kuwa cewa ta yi za ta taimakawa Mr. Macron ta fuskar samarwa faransawa ayyuka.
Emmanuel Macron, shugaban Faransar na 25 ya sami nasara gagaruma a babban zaben kasar na karshen mako inda Jamus ke alkawarin hada kai da shi wajen tabbatar da daidaito a nahiyar Turai.
A cewar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel dangantakar manyan kasashen na Turai, babban ginshiki ne a tsarin alakar Jamus da kasashen ketare musamman kan batutuwan da suka shafi hulda ta amana tsakaninsu.