WHO: Ba gaskiya a zargin corona da Amirka ke yi wa China
May 5, 2020![Tedros Adhanom Ghebreyesus Direktor WHO](https://static.dw.com/image/53211949_800.webp)
Talla
Hukumar ta ce babu wasu hujjoji kwakwara da ka iya tabbatar da zargi na cewar an kirkira cutar covid 19 a cikin dakunan harhada magunguna na garin Wuhan. Michael Ryan, shi ne daraktan kula da tsare-tsare na hukumar ta who yana mai cewa: "Ya ce mun saurari kwararru a kan sha'anin kimiya a karo da dama wanda suka tantance kwayoyin cutar na covid 19 kuma suka tabbatar da cewar cutar ba kirkirarta a ka yi ba don haka ba za mu taba yarda da wannan zargin ba".