1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar zaɓe ta fara bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a DRC

August 8, 2006

Hukumar zaɓe mai zaman kanta, a Jamhuriya Demokradiyar Kongo ,ta fara bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, da na yan majalisun dokoki, da a ka gudanar yau da kwanaki kimanin10, da su ka wuce.

A ƙalla 7, daga cikin cibiyoyin ƙidayar ƙuri´u 62, na ƙasar, sun liƙa sakamakon zaɓen yankunan su.

Shugaba Joshef kabila, ya yi wa saura yan takara fintinkau, tare da samun kashi fiye da 87 bisa 100, na yawan ƙuri´un da aka kaɗa.

Ɗan takara Azarias Ruberwa, na jami´yar RCD, ke sahu na 2 tare da kussan kashi 3 bisa 100, sannan sai Jean Pierre Bemba, ya samu kashi 1 bisa 100.

Saidai ya zuwa yanzu ,ba a bayyana sakamakon kuri´un s yankin arewacin ƙasar ba, inda a ake sa ran Jean Pierre Bemba zai taka rawar gani.

A halin yanzu, tunni yan takara sun fara ƙorafin tabka magudi da aringizon ƙuri´u, domin ba shugaba Josef Kabila damar zarcewa, tun zagaye na farko.