SiyasaAsiya
Hukumar zabe ta tuhumi tsohon fraministan Pakistan
January 3, 2024![Imran Khan](https://static.dw.com/image/67753835_800.webp)
Talla
Tsohon dan wasan Cricket din mai shekaru 71 Khanya shiga cikin rikicin siyasa da ta shari'a tun bayan da aka hambarar da shi a matsayin firaminista a watan Afrilun 2022.
Ba a dai sake ganin shi a bainar jama'a ba tun bayan da aka daure shi na tsawon shekaru uku a watan Agusta bisa laifin sayar da kayayyakin gwamnati ba bisa ka'ida ba, a lokacin da yake kan mulki daga 2018 zuwa 2022.
Lauyan shi Haider Panjutha, ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X cewar,humumar zabenkasar ta yanke wa Imran Khan hukunci ne ba tare da bayyanan lauyoyinsa ba.