1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kashi 86 na 'yan Chadi sun amince da sabon kundin mulki

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 25, 2023

Gwamnatin mulkin sojin kasar ce dai ta gabatar da bukatar amincewa da sabon kundin wanda aka kada kuri'a a ranar 17 ga watan nan na Disamba, a matsayin sharar fagen komawa tafarkin Dimokuradiyya

Hoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP/Getty Images

Hukumar zaben Chadi ta ce kudurin kaddamar da sabon kundin tsarin mulkin kasar ya samu amincewar kashi 86 cikin 100 na al'ummar kasar, ko da yake 'yan adawar gwamnatin sun nuna rashin gamsuwarsu da alkaluman da hukumar ta fitar.

Karin bayani:Sojojin Chadi za su raka na Faransa

Gwamnatin mulkin sojin kasar ce dai ta gabatar da bukatar amincewa da sabon kundin wanda aka kada kuri'a a ranar 17 ga watan nan na Disamba, a matsayin sharar fagen komawa tafarkin Dimokuradiyya.

Karin bayani:An kaddamar da gangamin yakin neman zaben raba gardama

Hukumar zaben ta Chadi ta ce kashi 63.75 na masu rajista ne suka kada kuri'ar, a zaben da 'yan adawa suka yi kiran a kauracewa, kuma sun nuna rashin amincewarsu da adadin wadanda suka fita rumfunan zaben.

Kotun Kolin kasar ce dai za ta tabbatar da sahihancin sakamakon karshe na zaben a ranar 28 ga wannan wata na Disamba.