1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An bayyana sakamakon zaben Ghana a hukumance

Suleiman Babayo AH
December 9, 2024

Hukumar zaben Ghana ya bayyana cikekken sakamakon zaben shugaban kasar Ghana da ya nuna John Dramani Mahama na jam'iyyar adawa ta NDC ya zama zababben shugaban kasar da ke yankin yammacin Afirka.

Ghana | John Mahama
John Dramani Mahama wanda ya lashe zaben shugaban kasar GhanaHoto: Seth/Xinhua/IMAGO

Hukumar zaben Ghana ta ayyana cikekken sakamakon zaben kasar, inda tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama mai shekaru 66 da haihuwa, yake kan gaba kuma ake ganin zai sake kadowa kan madafun iko, inda ya samu kaso 56.5 cikin 100, yayin da dan takarar jam'iyyar NPP mai mulki Mahamudu Bawumia ya samu kaso 41 cikin 100. Jean Mensa shugabar hukumar zaben ta tabbatar da haka lokacin da ta karanta sakamakon zaben.

Karin Bayani: Mataimakin shugaban Ghana ya rungumi kaddara

Mahama wanda ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar da ke yankin yammacin Afirka. Jam'iyyar NDC mai adawa ta Mahama take kan gaba a kujerun majalisar dokokin, yayin da jam'iyya mai mulki na NPP take matsayi na biyu, kuma tun farko dan takarar jam'iyya mai mulki Mahamudu Bawumia mataimakin shugaban kasa ya amince da shan kaye gabanin tattara sakamakon zaben a hukumance. Shi dai Shugaba Nana Akufo-Addo baya cikin 'yan takara saboda yana kammala wa'adinsa na biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.