Amon wuta na dutsen Etna a Italiya ya kawo cikas
July 23, 2024Talla
Dakatarda zirga-zirgar jiragen saman, ya biyo bayan da dutse mai amon wuta na Etna, ya fara bore. Dutsen na Etna wanda shi ne, mafi girma a nahiyar Turai, yanzu haka tokarsa ta mamaye sararin samaniyar yankin. Miliyoyin fasinjoji na yin safa da marwa ta wannan filin jirgin saman na Kataniya kowace shekara,daya daga cikin shahararrun wuraren yawon bude ido a Italiya.