1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin ƙasar Libiya sun sanar da kama Saif-Al-Islam

November 19, 2011

Gwamnatin wucin gadi ta Libiyan ta baiyana cewa an cafke mutumin da kotun Duniya da ke hukumta miyagun laifukan na yaƙi ke neman sa ruwa jalo

Saif Al-Islam GaddafiHoto: picture-alliance/dpa

Hukumomi a ƙasar Libiya sun ce sun yi nasarar cafke ɗan tsohon shugaban ƙasar wanda aka kashe a cikin watan jiya wato Saif Al Islam Gaddafi. Mininstan shari'a  na gwamnatin wucin gadi na ƙasar Mohammed Al-Alaqi shi ne ya ba da sanarwa cewa an kame Saif ɗin  a  yanki kudanci na ƙasar.

Wannan ba shi ba ne karo na farko da hukumomin Libiyan ke ba da sanarwa kama ɗan  marigayin kanal Muammar Gaddafin amma daga bisani  abin ya kasance ba gaskiya ba.Yanzu haka dai kotun Duniya da ke hukumta miyagun laifuka na yaƙi na neman saif al Islam ruwa a jalo tun a cikin watan Yuni da ya wuce, lokacin da ta ba da waranti sa akan tuhumar aikata kisan gila akan fararen fula .

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita        : Zainab Mohammed Abubakar