Hukumomin Algeria sun yi belin pirsinoni 2000
March 4, 2006Talla
Hukumomin Algeria, sun fara belin wasu daga mutanen da su ka tsare, a gigajen kurkuku, bayan sun tuhume su, da hannu a cikin ayukan ta´adanci.
Sun salami runkuni na farko, yamancin yau.
A halin yanzu,dubunan mutane ke tsare a gidan yarin Serkaj na birnin Algers.
Ranar laraba da ta wuce, hukumomin Algeria su ka alkawarta belin mutane 2000.
Tun watan Satumber da ya gabata, al´ummar ƙasar Algeria, ta ƙada kuri´a amincewa da saban kundin tsarin mulki, wanda ya tanadi ahuwa, ga dukan mutanen da ake tsare da su, da leffin ta´adanci , a sakamakon rikicin siyasa, da ya ɓarke a ƙasar Algeria,a shekara ta 1992, wanda kuma ya zuwa yanzu, ya hadasa mutuwar mutane dubu 150.