Hukumomin Iraki sun ce ana fatattakar mayakan IS
December 23, 2015Sojojin Iraki na ci gaba da fafatawa a kokarin karbe iko da ilahirin yankin Ramadi da ke zama tungar kungiyar IS da ke yammacin kasar ta Iraki. Babban jami'in 'yan sanda Hadi Rasij ya fada wa kamfanin dillancin labarun Jamus na DP cewa yanzu an 'yantar da fiye da kashi 90 cikin 100 na babban birnin wannan lardi daga hannun mayakan kungiyar IS. Shi kuma a nasa bangaren babban hafsan soji Othman al-Ghanemi ya fada wa tashar telebijin din kasar cewa nan da kwanaki kadan za a 'yantar da Ramadin baki daya.
Wani soja da ke filin ya nuna cewa "da yardar Allah za su samu galaba a kan kungiyar ta'adda ta IS."
Tun a ranar Talata dakarun gwamnati suka karfafa dannawa cikin tsakiyar birnin yayin da jiragen saman yakin sojojin kawance ke tallafa musu. Rahotanni sun ce mayakan IS kimanin 350 suna cikin birnin har yanzu.