1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

A Mali an kama wasu sojoji da yunkurin yin juyin mulki

Abdourahamane Hassane
August 10, 2025

Hukumomin kasar Mali sun kama akalla sojoji kusan 20 da ake zargin suna son hambarar da gwamnatin mulkin soji, wanda ita kanta ta hau karagar mulki ta hanyar juyin mulki sau biyu a shekara ta 2020 da 2021.

Hoto: AP Photo/picture alliance

Janar Abass Dembélé, tsohon gwamnan yankin  Mopti ta tsakiya kuma jigo a cikin sojojin, yana cikin wadanda aka kama.

Tun a shekara ta 2012 Kasar ta Mali ta fada cikin tashin hankali  sakamakon hare-hare daga kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da IS.

Sojojin da ke mulki sun kau da kai daga abokan kawancen kasashen Yamma, musamman tsohuwar uwargiyarsu Faransa, don karkatawa zuwa ga  Rasha da sunan neman cikakken yanci.