Hukumomin Masar sun tsare mutane da yawa karkashin dokar yaki da ta'addanci
December 26, 2013Gwamnatin Masar na kara matsa kaimi a kan kungiyar 'Yan uwa Musulmi, inda a wannan Alhamis ta tsare akalla mutane 38 bisa zargin kasancewa 'ya'yan wata kungiyar 'yan ta'adda. Bayan fashewar wani karamin bam da ya raunata mutum biyar a birnin Alkahira, Janar Abdel Fatah Al-Sisi wanda ya jagoranci juyin mulkin da aka yi wa shugaba Mohammed Mursi a cikin watan Yuli da ya gabata, ya ce kasar za ta tashi haikan don yakar ta'addanci. A ranar Laraba gwamnati ta ayyana kungiyar 'Yan uwa Musulmi a matsayin kungiyar 'yan ta'adda biyo bayan wani harin kunar bakin wake da ya halaka mutane 16 a yankin Nile Delta ranar Talata da ta gabata, wanda gwamnati ta zargi 'Yan uwa Musulmi da hannu a ciki, ko da yake kungiyar ta musanta zargin kana ta yi tir da harin.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman