Hukumomin Najeriya sun kama Igboho
July 20, 2021Kamen na Igboho dake kan hanyar tserewa zuwa kasar Jamus dai na zaman babbar nasara ga gwamnatin tarrayar Najeriya da ta yi nasarar cafke madugun awaren Biafra Nmandi Kanu a watan Yuni. Mutanen guda biyu dai na zaman na kan gaba a kokarin kare shekaru dari da doriya na rayuwar tarrayar Najeriyar sun kuma share tsawon lokaci suna gwada kwanji da fadar gwamnatin kasar.
To sai dai tuni muhawara ta yi nisa a cikin Najeriya bisa tasirin kamen nasu a kokarin mayar da awaren ya zuwa dogon suma.
Duk da cewar dai masu awaren guda biyu na jagorantar kungiyoyin biyu dai, da kamar wuya kamen nasu ya kai ga kare awaren cikin kasar dake dada fuskantar tasiri na siyasa.
Har ya zuwa yanzun dai alal ga misali, ana ta zanga zanga a manyan biranen kasashe kamar Ingila da Amurka da ma Isra'ila, sakamakon kama Nmandi Kanu dake hannun jami'an tsaron Najeriya.
Haka kuma an share wunin ranar Talata manyan jiga jigan kabilar yarbawa ta Igbohon na kartar kasar hana kasar ta Benin mika Igbohon domin fuskantar shari'ar a Najeriya wadda ke neman sa ruwa a Jallo.
Sai dai kuma kamen guda biyu a fadar Kabir Adamu na nuna irin tasirin Najeriyar da a baya ta mika masu awaren Kamaru, ta kuma samu goyon bayan 'yan uwanta na kasashen Africa.
An dai kame Igbohon dake neman tserewa ya zuwa Jamus a yayin da Kanu ya share lokaci yana kamfen din awaren daga Ingila