An kashe mutane 16 a gabashin Nijar
July 18, 2015Talla
Hukumomin tsaro a Nijar sun tabbatar da cewar aƙalla mutane guda 16 suka mutu a harin da Boko Haram ta kai a wani ƙauyen da ke cikin Boso da ke a gabashin ƙasar cikin jihar Diffa.
Gidan telbijan mallakar gwamnati na Nijar ɗin ya ambato magajin garin Bosso Bako Mamadou,yana mai cewar mayaƙan sun buɗe wuta a lokacin harin na ranar Larba a kan wasu jama'ar a lokacin da suke cikin yin sallah. Nan take mutane 15 suka cikka kana ɗaya ya mutu sakamakon raunikan da ya samu daga bisani yayin da wasu huɗu suka jikkata.