Hukumomin Pakistan sunj anye dokar daurin talala a kan Bhutto
November 9, 2007Talla
Gwamnatin ƙasar Pakistan, ta janye dokar ɗaurin talala da ta yi wa tsofuwar Praminista Benazir Bhutto.
Kakakin gwamnatin Tariq Azeem, ya ce cemma hukumomin sun ɗauki wannan doka da zumar kare lafiyar Bhutto, da ke fuskantar barazanar harin ta´danci.
Ya ce a lokacin da wasu yan takife su ka abka mata hari, ranar 18 ga watan Oktoba da ya wuce, ta zargi gwamnati da nuna sakaci wajen tsaran lafiyar ta.
A saboda haka,gwamnatin ta yanke shawara hana mata halartar taron gangamin da jam´iyar ta, ta shirya.
Saidai a ɗazunan, gwamnatin Islamabad, ta bayyana janye wannan doka.
Ƙasashen Dabam-dabam na dunia, wanda su ka haɗa da Amurika, Jamus da France ,sun yi Allah wadai ga matakin da shugaba Pervez Musharaf ya ɗauka na ɗaurin talala ga Benazir Bhutto.