Hukumomin Saudiyya sun kame ´yan tawayen Islama akalla 30
June 24, 2006Talla
Majiyoyin tsaro a kasar Saudiya sun ce dakarun tsaron kasar sun kame akalla mutane 30 da ake zargi sojojin sa kai ne na Islama wadanda ke kai hare hare a fadin daular baki daya. Wata sanarwa da ma´aikar cikin gida ta bayar ta nunar da cewa mutanen da aka kaman na da alaka da kungiyoyi masu matsanancin kishin Islama. Hakan dai ya zo ne kwana guda bayan an halaka ´yan ta´adda 6 da dan sanda daya a wata musayar wuta da aka yi a Riyadh babban birnin kasar. ´Yan takife masu alaka da kungiyar al-Qa´ida na fatatawa da nufin kifar da gwamnatin mulkin mulukiya da Amirka ke goyawa baya.