Hukumomin Sudan sun saki jagoran 'yan adawa
June 15, 2014Talla
A wannan Lahadi, hukumomin kasar Sudan sun saki madugun 'yan adawa na kasar Sadiq al-Mahdi, kamar yadda ministan yada labarai na kasar Yasser Youssef ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Cikin tsakiyar watan jiya na Mayu aka cafke tsohon firamnistan bisa zargin zagon kasa wa tsarin mulki, bayan da ya zargi gwamnatin kasar da hannu cikin tashin hankalin da ya tagaiyara fararen hula a Lardin Darfur. A cikin shekarar 1989 Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan ya jagoranci kifar da zababbiyar gwamnatin firaminista Sadiq al-Mahdi.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe