Hukunci bisa laifin yiwa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa
April 17, 2012A wannan Talatar ce wata kotun Birtaniya ta yankewa James Ibori, tsohon gwamnan jihar Delta a Najerya hukuncin ɗaurin shekaru 13 bayan da ya amsa laifin yin almubazzarancin kuɗin daya kai Fam na Ingila miliyan 50 wato kwatankwacin dalar Amirka miliyan 79, wanda ke zama ɗaya daga cikin manyan laifukan safarar kuɗi ta haramtacciyar hanya da aka yi shari'ar ta a Birtaniyar.
James ibori, wanda fitaccen ɗan jam'iyyar PDP dake mulki a Najeriya ne, a yanzu shi ne fitaccen ɗan siyasar ƙasar na baya bayannan da aka yankewa hukunci bisa cin hanci da rashawa bayan daya yi shekaru 8 na mulki a matsayin gwamnan jihar Delta. Yunƙurin baya na gurfanar da shi da kuma yanke masa hukunci a Najeriya dai ya ci tura.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar