140510 Iran USA Sanktionen
May 14, 2010A halin da ake ciki yanzu haka ƙasar Amirka na bakin ƙoƙarinta wajen janyo hankalin kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya domin ya ɗora wasu sabbin matakai na takunkumi akan ƙasar Iran dangane da shirinta na nukiliya. Ana dai yi tababa ne a game da cewar ƙasar ta Iran tana neman fakewa da guzuma ne domin ta harbi karsana, inda take iƙirarin amfani da nukiliya don samar da makamance, amma a fakaice tana ƙoƙari ne da ƙera makaman ƙare dangi.
Ita dai ƙasar Iran ta sha musunta wannan zargin da ake yi mata, amma kuma a ɗaya ɓangaren, ta sha yin cikas ga jami'an bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya wajen binciken tashoshinta na nukiliya. Sai kuma Amirka na buƙatar goyan baya daga ƙasashen Rasha da China domin cimma manufar ta tsaurara takunkumi kan ƙasar Iran. A dai baya-bayan nan a duk lokacin da shugaba Barak Obama ke batu a game da tsaurara matakan na takunkumi akan Iran sai ka ga kamar dai yana lalube ne a cikin duhu:
Ya ce:Takunkumi ba wani mataki ne na dabo ba, amma mai yiwuwa ya taimaka a samu wani canji a take-taken wata ƙasa kamar Iran.
Wajibi ne Iran ta lura da gaskiyar cewa ci gaba da aiwatar da shirin nata na nukiliya ka iya zame mata alaƙaƙai ƙadangaren bakin tulu. Kasancewar dai matakan da aka ɗauka kan ƙasar a zamanin baya ba su tsinana kome ba, jami'ai a fadar mulki ta White House ke tattare da imanin cewar tsaurara waɗannan matakai mai yiwuwa ta taimaka kwalliya ta mayar da kuɗin sabu bisa manufa. Wannan kuma shi ne abinda Amirka take yayatawa. An dai yi nuni da cewar ƙasashen Rasha da China, waɗanda bisa al'ada suke adawa da maganar tsaurara takunkumin kan Iran a yanzu sun fara nuna sassauci. Amma fa duk da haka akwai ayar tambaya a game da ko shin wannan sassaucin da ƙasashen biyu suka nunar zai taimaka a tsaurara matakan takunkumi kan Iran kamar yadda Amirka ke buƙata. Domin kuwa ba a taɓa amincewa da wata shawara akan wani ƙuduri ba tare da gindaya sharuɗɗa ba. Ga dai abin da mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Segej Rjabkow yake cewa:
Ya ce:Ba zata yiwu a ɗauki wani matakin ladabtarwa akan ƙasar ko akan al'umarta, kome girman laifinta.
Ita ma China ga alamu ba ta sha'awar tsaurara wa fadar mulki ta Tehran. Domin kuwa Iran ce a rukuni na uku wajen sayarwa da ƙasar China man fetir kuma ƙasashen biyu na shawarar kafa wani bututu na mai tsakaninsu. Ta la'akari da haka ƙasar ta China ba zata so ta ga wani abin da zai yi barazana ga wata muhimmiyar ƙawar dake taimaka mata da makamashi ba, in ji Dr. Ivan Oelrich daga gamayyar masana kimiyya ta ƙasar Amirka.
Ya ce:Na yi imanin cewar ko ba daɗe ko ba-jima maganar tsaurara matakan takunkumin, kamar yadda ake yayatawa a Washington, zata sha ruwa.
A dai halin da ake ciki yanzun Iran na fama da matsalar hauhawar farashin kaya. Sai dai kuma ƙwararrun masana al'amuran ƙasar sun ce wannan rikicin ba ya da nasaba da takunkumin da aka ƙaƙaba mata, sai dai rashin iya gudanarwa na mahukuntan ƙasar, shi ne aikin hin ummal'aba'isin wannan matsala.
Mawwallafi: Ahmed Tijani Lawal Edita: Yahouza Sadissou Madobi