ICC kan saka yara a aikin soja
October 11, 2016![Internationaler Strafgerichtshof in Den Haag ICC](https://static.dw.com/image/15811722_800.webp)
Wannan zama na kotun ta ICC da zai ci gaba har ya zuwa ranar Alhamis, zai bai wa alkallan kotun damar sanin irin adadin kudadan da ta kamata a bai wa ko wane daya daga cikin yaran da aka yi amfani da su a matsayin sojoji, wadanda madugun 'yan tawaye na wancan lokaci Thomas Lubanga ya saka su ciki a shekara ta 2002 da 2003.
A kalla dai an ware kudi kimanin miliyan daya na Euro kan wannan batu daga cikin asusu na musamman da aka tanada kan iri-irin wannan matsala kamar yadda yarjejeniyar birnin Roma wadda ta tanadi kirkiro da wannan kotun ta kasa da kasa ta ICC ta tsara.
A shekara ta 2015 alkallan kotun sun amince cewa Thomas Lubanga da aka yanke wa hukunci a shekara ta 2012, shi ne zai biya diyyar wadan nan yara da ya dauka a matsayin sojojin yaki, inda kawo yanzu da dama daga cikinsu ke fuskantar wariya da tsangwama daga al'umma.