Hukunci kan 'yan kungiyar FDLR ta Ruwanda
October 3, 2015Za mu fara sharhunan jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka ne daga nan Jamus, inda a farkon mako wata kotu a birnin Stuttgart da ke kudancin kasar Jamus ta yanke wa wasu tsoffin 'yan tawayen Ruwanda hukuncin daurin shekaru barkatai a gidan maza.
A labarin da ta buga mai taken hukuncin mai tattare da rudani, jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi:
A ranar Litinin babbar kotun jiha a birnin Stuttgart ta kawo karshen zaman sauraron shari'a mafi tsada a tarihin Jamus tare da yanke hukuncin da ya ci karo da mabanbantan ra'ayoyi. Kotun ta samu mutane biyu mazauna a Tarayyar Jamus da laifin tallafa wa 'yan takifen kabilar Hutu na kungiyar FDLR da ke yaki a Kwango. Sabanin fatan da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka yi, kotun ba ta yanke wa shugaban FDLR Ignace Muwarnashyaka hukunci a matsayinsa na mai ba da umarni ga kungiyarsa da ta aikata laifin yaki a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ba. Sannan mataimakinsa na farko Straton Musoni ya bar harabar kotun a matsayin 'yantaccen mutum domin ya rigaya ya yi kashi biyu bisa uku na yawan hukuncin da aka yanke masa, a gidan wakafi. An yanke wa shugaban hukuncin daurin shekaru 15 shi kuma mataimakin nasa ya samu shekaru takwas. Dukkansu biyu dai sun shafe shekaru shida a Jamus.
Halin rashin sanin tabbas a Burkina Faso
Gurguwar dabara ta hafsan soji inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai cewa makonni biyun da suka gabata sun kasance masu damuwa da kuma daure kai ga kasar Burkina Faso.
Ta ce da farko an yi juyin mulki, bore ya barke wanda aka murkushe shi da karfin tuwo. A karshe sojoji sun ja daga sun nemi masu juyin mulki su mika wuya, amma jagoransu Janar Gabriel Diendere ya jira matakin kungiyar AU da kuma kungiyar ECOWAS, inda bayan kai komo a fannin diplomasiyya ya amince ya sake mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya. Sai dai har yanzu ana cikin rashin tabbas a kasar, amma duk da haka dai wannan juyin mulki da bai dore ba, ya karfafa tafarkin demokradiyya maimakon raunata shi.
Anti-Balaka da tashe-tashen hankula a Bangui
Tashin hankali ya girgiza birnin Bangui inji jaridar Die Tageszeitung inda ta kara da cewa 'yan takifen Anti-Balaka wadanda a bara suka fatattaki Musulmi daga yankuna da dama na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
'Yan takifen na kungiyar Anti-Balaka sun kai farmaki kan tawagar Majalisar Dinkin Duniya da kuma gwamnatin rikon kwarya.
Rahotanni sun yi nuni da cewa sakamakon wannan tashin hankalin, ya sa an kwashe ma'aikatan agaji na kasa da kasa zuwa tudun mun tsira ko kuma sun gudu zuwa cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya. An dai wasashe ofisoshi da gidajen kungiyoyin agaji da yawa. Jaridar ta kara da cewa yanzu kam fatan da ake na samun zaman lafiya da kuma shirya zabe nan gaba kadan a kasar, ya bi iska. A karshen mako mayakan kungiyar Anti-Balaka sun kwace iko da yankuna da dama na babban birnin kasar wato Bangui.