1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daurin rai-da-rai ga mutanen da suka kashe zabiya

Kaliza Mirriam Khadijah Ahmad Rufai(AMA)(Lateefa)
June 28, 2022

Babbar kotu a kasar Malawi ta yanke hukunci mai tsanani ciki har da daurin rai-da-rai ga mutane tara, bayan ta kama su da laifin yi wa wani matashi zabiya kisan gilla a shekara ta 2018.

Ali Faque Albino-Musiker in Mosambik
Hoto: Carlos Litulo

Kotu ta yankewa mutane biyar hukuncin daurin rai da rai bisa samun su da laifin kashe wani mutum mai suna Mcdonald Masambuka, wannan kuwa duk da yankewa Fada Thomas Muhosha da ke zaman limamin Cocin Katolika hukuncin shekaru 30 a gidan yari tare da horo mai tsanani bayan kama shi laifin safarar sassan jikin dan Adam, kotu ta taba yankewa mutane 12 hukunci bayan samunsu da laifuka kala bakwai masu nasaba da kisan Masambuka, matakin da ya samu yabo da guda daga Byson Makolopa-APAM wakilin kungiyar zabiya ta kasar Malawi.

"Gaskiya ne mun rasa abokinmu, amma mun ji dadi tunda an kama masu laifin, wannan ma ya isa, muna fatan wannan hukunci da aka yanke zai zama izina ga masu niyyar aikata irin wannan laifin. Mutane a gida ma za su ji dadi idan muka koma musu da wannan labari."

Hoto: DW/M. Mueia

Lauran da ke kare masu laifi Masauko chamkakala ya bayyana cewar za su daukaka kara idan sun so, saboda rashin gamsuwa da shari'ar, yana cewa hujjojin da aka bayar na tuhumarsu ba sa daga cikin laifukan da suka amsa. "Dole mu fara zama mu fahimci tsarin wannan kotun, mu tattauna da wadan da muke karewa, sannan mu yanke hukunci akan daukaka kara ko akasin hakan a kotun koli." Abinda ya faru shine, marigayi Masambuka ya samu yaudara daga dan uwansa da abokanan sa kan cewar sun samo mishi mata. Dan uwanshi Cassim shi ne yayi kaman yana magana da matar da suka ce sun samar mashi, da haka ne suka ja ra'ayinsa kan ya je su ga juna, sun yi amfani da wannan dama suka kashe shi kamar yadda ya amsa laifin shi.

 
Mai shari'a a kotun koli Dorothy Kamanga, wanda ta taimaka kan kwatowa marigayi Masambuka yanci, ta kira dan uwansa a matsayin mayaudari da ya ci amanar dan uwanshi aka kashe shi a gabanshi mai makon ba shi kariya. Anyi wa Masambuka kisan gilla ne da daddare a wata makabarta, kuma an tsinci gawarsa a binne a wurin shakatawa.