1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunci mai tsauri zai rage yawan fyade

June 18, 2014

Kungiyoyin da ke da rajin kare yara mata na yunkurin ganin mahukunta sun samar da dokar da za ta tanadi hukunci mai tsauri ga wadanda ke musgunawa kananan yara

Kinder in Nigeria
Hoto: cc-by-nc-nd 2.0/World Bank Photo Collection

Kungiyoyon Mata a Tarayyar Najeriya sun bukaci gwamnatin kasar da ta hanzarta Kaddamar da doka mai tsananin gaske don hukunta masu yiwa kananan yara fyade, da zumar hana ci-gaban lalata kananan yara mata 'yan kasa da shekaru 5

A yanzu haka dai a kullun ana samun karuwar rahotannin fyaden kananan yara mata a Tarayyar Najeriya sakamakon rashin kaddamar da tsayayyar dokar hukunta masu lalata rayuwar daruruwan yara maza da mata a cikin kasar.

A saboda haka ne wata hadaddiyar kngiyar mta Lauyoyi ta kasa tare da hadin guiwar sauran kungiyoyin kare hakkin yara mata su ka ga cewa lokaci ya yi na daukar dukkanin matakan da suka cancanta don dakile ci-gaban musgunawar da ake wa yara mata a cewar dai barista Adama Hamma tsohuwar shugaban kungiyar mata lauyoyi ta kasa.

Hoto: Earth Day Network

Yunkurin dakile matsalar fyade tsakanin yara

"Mu na samun koke-koken alumma a kowace rana gane da yadda ake yiwa kananan yara mata fyade akai-akai, ta ce kananan yara a Najeriya na cikin mawuyacin halin rayuwa, ta ce babban abun da mu ke so daga hannu iyayen yara shi ne, da zarar an yi wa 'ya'yan fyade su je asibiti daga nan kuma sai su wuce zuwa koto don koto ta dauki hukunci akan wanda ake zarji da yin lalaci da yara,tace idan ba ku manta ba, a shekaru 3 da suka gabata, akwai wani mutun da ake zargin sa da lalata wasu kananan yara, bayan mun kammala binciken mu,mun gano cewa bayan lalata wadannan yara guda 3,ya kuma yada masu zutar HIV/AID"


Sau tari dai wadannan yara da aka yi masu fyade, sukan kamu da kwayar cutar HIV da wasu cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyoyin jima'i da ke bata rayuwar yara mata, bugu da kari rahotanni sun nunar da cewa wasu iyayen yara da damar gaske kan ji tsoran kai kara kotu saboda irin tsangwamar da yarinyar za ta taso da shi ,domin wasu lokuta kuma jami'an tsaro ne ke sako wadanda aka kama sunyi wa kananan yara fyade,inda suke dawuwa cikin gari,suna ci-gaba da yin barna


Ayyukan kungiyoyin tallafawa yara

Hajiya Hafsat Baba ita ce dai shugaban wata kungiyar da ke kula da mata da kananan yara a Najeriya da ke ganin cewa lallai dai kam lokaci yayi da gwamnatin Kasar za ta dauki matakan kawo karshen ci-gaban musgunar da ake yi wa kananan yara

"Muna bukatar ganin an kaddamar da Dokar da za ta sanya iyayen yara da kungiyoyin masu zaman kansu, sun sami kwanciyar hankali,tace rashin kaddamar da wannan dokar don hukunta masu aikata 'dan yan aiki akan kananan yara, ya kawo ci-gaba ga harkokin inganta rayuwar yara mata a cikin birane da karkara, a saboda haka hanyar dakile ci-gaban zaluncin da ake yi wa wadannan yara mata ita ce na kaddamar da dokar hukunci dan tabbatar da adalci"


Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Pinado Abdu Waba