1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hukuncin babbar kotun tarayya kan masarautar Kano

Nasir Salisu Zango SB
June 20, 2024

Kotun tarayya da ke zama a Kano ta ce nadin Muhammad Sunusi a matsayin sarki bai nadu ba. Alkalin ya ce dokar rushe sarakuna ta jihar Kano tana nan amma masarautun ba su rusu ba, lamarin ya sake jefa mutane a rudani.

Bikin Sallah a Najeriya
Bikin Sallah a NajeriyaHoto: Marvellous Durowaiye/REUTERS

Hukuncin dai ya zama tamkar tufka aka yi da warwara, domin a waje guda alkalin kotun Justice Liman ya ce nadin da aka yi wa Muhammad Sunusi na biyu da rushe masarautun Kano bai yuwu ba, amma a waje guda alkalin ya shiga sadara ta gaba daga cikin kunshin hukuncin inda yake cewar dokar da majalisar dokokin jihar Kano da ke Najeriya ta yi kan masarautun tana nan daram lamarin da ya zama ga koshi ga kwanan yunwa, kuma wannan hukunci ya ci gaba da jawo fassara me harshen damo daga lauyoyin bangarorin biyu in da Barrista M A Lawal tsohon atoni janar na jihar Kano ke cewar hukuncin kotun na nufin cewar, har yanzu Mai Martaba Aminu Ado Bayero shi ne halastaccen sarkin Kano. To amma a ra'ayin Barista Badamasi Gandu lauya mai zaman kansa wanda kuma ke da wulaya ga gwamnatin Kano cewa ya yi dokar ba ta sauke Muhammad Sunusi na biyu ba kuma shi a fahimtarsa shi ne halastaccen sarki.

Karin Bayani: Sarki Sanusi ya jagoranci sallar Juma'a a Kano

Yanzu haka dai babban abin da ke damun mutanen jihar Kano shi ne yadda aka dauke hankali daga matsalolin jihar aka koma kan batun wannan turka-turka har takai 'yan daba sun samu dama suna sa ran mutane saki ba kaidi, domin kwanaki biyu da suka gabata wani shugaban bijilanti 'yan dabar suka kai wa farmaki gida suka halaka shi haka kuma yan dabar na cigaba da yin zuga da tsakar rana suna saran mutane, lamarin da ya sa zauren hadin kan malaman Kano ke kira da a yi tunani a zauna lafiya, Dr Saidu Ahmad Dukawa shine sakataren zauren ya ce kamata ya yi shugabannin da abin ya shafa su yi hattara.

Babban abin da ke ba da mamaki shi ne yadda ake baje 'yan daba suna gadin gidajen sarakunan a wani yanayi da mutane ke zargin shine ya kara jawo tabarbarewar harkokin daba a Kano.