Kotu ta kama kawun Bashar al-Assad d laifi
June 17, 2020Talla
Wata kotu a birnin Paris ta yanke hukuncin daurin gidan yari har na tsawon shekaru hudu ga Rifaat al-Assad wani kawun shugaban kasar Siriyya Bashar al-Assad
Sai dai ko baya ga hukuncin zaman gidan yarin, kotun ta kuma yanke hukuncin karbe kaddarorin da Rifaat al-Assad mai shekaru 82 a duniya, ya tara wadanda aka kiyasta sun kai euro miliyan 90, to amma bisa rashin lafiyarsa an yi shara'ar ce ba tare da halartar Rifaat a gaban kotun ba.
Tuni dai lauyoyin da ke kare shi suka yi kakkausar suka ga matakin suna cewar ba a yi masa adalci ba kuma za su daukaka kara.