Hukuncin daurin rai da rai a Masar
February 4, 2015Talla
Daga cikin wadanda wannan hukunci ya shafa dai har da wanda ya jagoranci gangamin adawa da gwamnatin ta Mubarak Ahmed Douma. Wani jami'in gwamnatin kasar ta Masar ne ya tabbatar da yanke wannan hukunci inda ya ce an kuma yankewa wasu 39 da aka samu da kanan laifuka hukuncin daurin shekaru 10 a gidan kaso kowannen su. Hukuncin wanda za a iya daukaka kara a kansa, na zaman mafi tsauri da kotun ta yanke a kan masu fafutukar da ba na kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Masar din ba. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin jagoran juyin mulkin kasar da a yanzu ya dare kan karagar mulki bayan gudanar da zabe Abdel Fattah al-Sisi ke tsaka da murkushe 'yan adawa.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu