Masar: Hukuncin kisa kan mutane 37
March 2, 2020Talla
Hisham el-Ashmawi da kotun ta kwatanta a matayin shugaban kungiyoyin tada kayar baya, tsohon shugaban bataliyar sojojin da ke biyayya ga Janar Khalifa Haftar ne a kasar Libiya.
Sauran mutanen da aka yanke wa hukuncin kisan, suna cikin mutane 200 da gwamnatin Masar ke zargi da kai hare-hare kusan 50 da ya yi sanadiyar rayukan fararen hula da 'yan sanda.
Masar ta sha fuskantar hare-haren daga kungiyoyin 'yan tawaye da suka addabi arewacin Sinai da yankunan da ke yammacin Hamada. Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil Adama na sukan irin wannan kisan da gwamnatin ke yi.