Hukuncin kisa kan wasu sojojin Sudan
August 6, 2021Talla
Kotun da ke Khartoum ta yanke hukuncin kisa kan wasu dakarun Rapid Support Force(RSF) bayan da aka same su da laifin kisan masu zanga-zanga a lokacin da guguwar sauyi ta kada a kasar, shekaru biyun da suka gabata.
Alkalin kotun Ahmed Hassan al-Rahma ya ce, ko kadan, bai dace a yi wa dalibai da suka fito zanga-zangar lumana irin wannan kisan gillar ba. Ya soki kisan da kuma ya ce, tsantsan rashin imani ne.
A shekarar 2019, zanga-zangar nuna adawa da mulkin Oumar al-Bashir ta barke saboda karancin abinci da man fetur a kasar. Kimanin mutane 128 alkaluma suka nunar sun mutu, daga kashe-kashen da aka zargi dakarun RSF da hambararren shugaban ya kafa a shekarar 2013 da aikatawwa. An dai nuna yadda aka yanke ta kafar talabijin din kasar.