Hukuncin Kotun ICC akan Lubanga
March 14, 2012Tun a cikin watan maris na shekara ta 2009 ne aka fara sauraren ta bakin masu ba da shaida a zauren kotun ta The Hague, inda wani tsofon ɗan tawayen yayi nuni da cewar:
"Na gani da ido na yadda aka harbe wani matashi har lahira lokacin da yake ƙoƙarin guduwa. Manufar matakin shi ne domin ya zama darasi ga sauran matasa na cewar ba wanda zai iya tserewa daga aikin sojan dole. An kashe shi akan ido na."
Shi dai tsofon ɗan tawayen dake ba da shaida, an jirkita muryarsa ne saboda a kare lafiyarsa. Shi kansa tsofon madugun 'yan tawayen Thomas Lubanga Dayilo, dake da shekaru 51 da haifuwa ya hallara a zauren shari'ar a wannan zaman da aka yi a watan maris na shekara ta 2009. A dai shekara ta 2006 ne gwamnatin ƙasar Kongo ta cafke shi ta kuma danƙa shi hannun kotun ƙasa da ƙasa kan miyagun laifuka na yaƙi dake The Hague, sannan aka fara cin shari'arsa a shekara ta 2009.
Ana zargin Lubanga da laifin yi wa ɗaruruwan yara ƙanana ɗamarar makamai a Ituri ta gabashin Kongo tsakanin shekara ta 2002 da shekara ta 2003, domin yi wa ƙungiyarsa ta 'yan tawaye aikin soja ala tilas. Da yawa daga cikin yaran ma dai ba su cika shekara 15 da haifuwa ba. Ya tilasta musu yin kashe-kashe na gilla da kuma yin lalata da su. Shari'arsa dai ita ce ta farko da aka gabatar da kotun ta ƙasa da ƙasa dake The Hugue dangane da tilasta wa yara ƙanana aikin soja. An ji daga bakin babban mai ɗaukaka ƙara a kotun Luis Moreno-Ocampo yana mai bayani da cewar:
"Muhimmin abu gare ni, shi ne hukunci. Domin maganar ta shafi yara ne, waɗanda aka ba su horo na kisa."
Sau biyu ana ɗage zaman shari'ar akan Lubanga. Dalili shi ne ƙorafin da kotun tayi na cewar babban mai ɗaukaka ƙarar da abokan aikinsa ba su gabatar da wata takamaimiyar shaida ba kuma suna rufa-rufa a game da masu ba su rahotanni a airce. A ganin alƙalan kotun wajibi ne lauyoyin Lubanga su samu cikakkun bayanai ta yadda shari'ar zata gudana a cikin adalci. Kuma ko da yake an ba wa lauyoyin dukkan kundayen bayanan da aka tara, amma ba a bayyana sunayen masu ba da shaida ba.
A taƙaice dai, kamar yadda ƙungiyoysin kare haƙƙin ɗan Adam suka nunar, hukuncin da aka yanke akan Lubanga zai share hanyar gurfanar da sauran waɗanda ake zargi da irin waɗannan laifuka a gaban kotun, waɗanda suka haɗa da tsaffin jami'an gwamnatin Kenya da Cote d'Ivoire da kuma waɗanda tuni aka ba da umarnin cafke su kamar shugaba Omar Al-Bashir na Sudan da Saif al-Islam Ghaddafi, ɗan tsofon shugaban Libiya Muammar Ghaddafi.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu