1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jaridun Jamus: Hukunicin Kabila ya dau hankali

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
October 3, 2025

Yanke hukuncin kisa kan tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Kwango Joseph Kabila da rikicin Sudan, sun dauki hankulan jaridun Jamus.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Goma | Joseph Kabila | Hukuncin kisa
Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Joseph Kabila Hoto: Jekesai Njikizana/AFP

"An yanke wa tsohon shugaban Kwango Joseph Kabila hukuncin kisa a bayan idansa," a cewar jaridar die tageszeitung. Jaridar ta ce: Kotun kolin sojoji a Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ta yanke wa tsohon shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa. A karshen shari'ar da aka yi ta tsawon watanni biyu, an yi ta ba tare da yana nan ba.

An samu tsohon shugaban da laifukan yaki da shirya tawaye da makami da kuma cin amanar kasa, a cewar alkalan. Mai shekaru 53 a duniyar, shi ne shugaban hadakar 'yan tawayen AFC da M23 na gabashin Kwangon da ke son hambarar da shugaban kasar Félix Tshisekedi. Sai dai kuma 'yan tawayen M23 ba Kabila ne ke jagorantar su ba, an kafa su ne don yin adawa da shi kuma har yanzu ba su amince da shi ba.

Zanga-zangar adawa da gwamnati mafi girma a MorokoHoto: AFP

"Zanga-zanga mafi girma da aka yi a Maroko cikin shekaru masu yawa saboda gina filayen wasan kwallon kafa." Wannan shi ne taken labarin da jaridar Welt Online ta wallafa a kan boren adawa da gwamnati mafi girma da matasa suka fara tun a karshen mako. Gina sababbin filayen wasanni domin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ta 2030 da kuma rashin yanayin tsarin kiwon lafiya mai kyau a kasar, su ne musabbabin zanga-zangar.

Maroko ta tsinci kanta cikin zanga-zanga

Jaridar ta ce: Matasa sun yi arangama da 'yan sanda a wannan gangami da ya kasance zanga-zangar adawa da gwamnati mafi girma a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan a manya garuruwan kasar Maroko 10. Masu zanga-zangar, sun yi tir da abin da suke ganin cewa gwamnati ta mayar da hankali a kai. Kaiai tsaye sun alakanta tsarin kiwon lafiyar kasar ta maroko da ke kara durkushewa da kuma makudan kudin da aka zuba cikin harkar shirye-shiryen gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ta 2030, suna rera taken " filayen wasa suna nan amma ina asibitoci?"

Dubun-dubatar mutane ne suka tsere daga SudanHoto: Khaled el fiqi/dpa/picture alliance

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta nata sharhin mai taken: "Fata na gari a kan rikicin Sudan". Jaridar ta ci gaba da cewa: Amurka na jagorantar wani sabon shiri na kawo karshen kashe-kashen da ake yi a kasar ta Afirka, wanda ke da nufin yin tasiri da hadin gwiwar kasashen Larabawa. Wannan dama ce, to amma bangarorin da ke rikicin za su amince?

Ko yakin Sudan zai kawo karshe

Washington ta hada gwiwa da kasashen Larabawa uku, Masar da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa wajen ganin an cimma kawo karshen wannan rikici da hankalin duniya ba ya kansa. A tsakiyar watan Satumba, wannan gamayya ta kasashe hudu ta ayyana wasu ka'idoji da nufin dakatar da yaki da kisa a Sudan. An dai shafe shekaru biyu da rabi, ana gwabza yaki tsakanin manyan jagororin sojin kasar biyu da ke neman madafun iko.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani