EU da Iran sun amince da kasuwanci na musamman
September 25, 2018Talla
Ministocin harkokin waje na Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha da China da Iran sun bayyana tsari da sunan "kadami mai aniya ta musamman" da zai taimaka masu wajen ci gaba da kasuwanci ta halastacciyar hanya da kasar ta Iran.
Yarjejeniyar da aka kulla da Iran dai na da buri ne na ganin mahukuntan na Tehran ba su ci gaba da shirinsu na kera makamin nukiliya ba, sai dai Amirka ita kadai a watan Mayu ta janye hannunta daga yarjejeniyar ta 2015, saboda abin da Shugaba Donald Trump ya kira akwai wasu batutuwa da yarjejeniyar ba ta hada da su ba wadanda suka shafi Amirkar da kawayenta.