1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron koli na China da Afirka na kara samun karbuwa

Binta Aliyu Zurmi AH
September 4, 2024

An bude babban taron kolin China da kasashen Afirka 50. Gabannin taron shugaban China Xi Jingpig ya gana da shugabanni da dama na Afirka ciki har da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

Hoto: Tanzania presidential communication unit

 Taron shine karo na tara da mahukuntan Beijing suka gayyato shugabanni Afirka 50. Manyan batutuwan da za su mamaye babban zauren taron na China da Afirka akwai batu na hadin kai da saka hannayen jari da ma lalubo hanyoyin cimma yarjejeniya a kan sauyin yanayi da makamashi gami da batun na fasahar zamani. Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da Shugaba Xi Jingping, inda mahukuntan na China suka sha alwashin karfafa gwiwar manyan kamfanonin kasar saka hannayen jari a Najeriya ta hanyar samar da masana'antu da bunkasa fannin makamashi da albarkatun ma'adanai.

Samia Suluhu Hassan shugabar Zambiya tare da Xi JinpingHoto: Tanzania presidential communication unit

A jawabinsa yayin ganawa da shugaban Najeriya, Xi Jingpin ya bayyana muhimmancin Najeriya a irin wannan taro da ma karfin tasirinta a nahiyar ta Afirka, kazalika ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen amfani da wannan damar don yin waiwaye a kan irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da ma nahiyar ta Afirka, " Tun bayan kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu sama da shekaru 50 da suka gabata, China da  Najeriya sun kasance masu aiki tare da girmama juna da ma aiki tare don samun kyakkyawan hadin kai. A wannan karon za mu sanya sabbin sauye-sauye a dangantakar da ke tsakanin China da Afirka."

Xi JinpingHoto: Sergei Savostyanov/POOL/AFP/Getty Images

Najeriya ita ce kasar da ke da yawan bashin China a kanta, a wani rahoton da ofishin kula da basussukan Najeriya ya fidda, ya zuwa karshen watan Maris China na bin Najeriya bashin sama da dala biliyan biyar. Daga cikin manyan kamfanonin da suka yi alkawarin saka hannayen jari a Najeriya, akwai kamfanin laturoni na Huawei wanda shugaba Tinubu ya kai ziyarar gani da ido kuma ya tabbatar da alkawarin kamfanin na samar da babban kamfanin makamashin hasken rana.

Da yake tsokaci kan dangantakar Najeriya da China, shugaba Tinubu ya yi jawabi kamar haka."Muna fatan wannan dangantaka ta China da Najeriya da ta jima a karfafata ta shirinmu na kasuwanci da bunkasa tattalin arziki,mun yi imanin cewa ka gyara tattalin arzikin China kuma mu ma muna kan wannan hanyar"

Hoto: Tanzania presidential communication unit

To sai dai taron na zuwa ne a daidai lokacin da kasashe da dama da ke halarta suke fama da rugujewar tattalin arziki a kasashensu. Kasashe irinsu Tanzaniya da Zambiya da Kenya sun isa zauren taron ne da kokon bararsu. A gefen taron kasashen Tanzaniya da Zambiya sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar samar da layin dogo da zai rinka sintiri a tsakanin  kasashen.