1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Huldar cinikayya a tsakanin Turai da China

November 21, 2013

China da EU sun fara taron kulla yarjejeniyar da ta shafi harkokin zuba jari da na kasuwanci a tsakaninsu.

China's Premier Li Keqiang (4th L) meets with European Commission President Jose Manuel Barroso (3rd R) and European Council President Herman Van Rompuy (2nd R) at the Great Hall of the People in Beijing, November 21, 2013. REUTERS/Kim Kyung-Hoon (CHINA - Tags: POLITICS BUSINESS)
Hoto: Reuters

China da Kungiyar Tarayyar Turai sun fara tattauna hanyoyin kulla yarjejeniyar da ta shafi harkokin zuba jari, wadda shugaban tarayyar Turai ya kwatanta da cewar, muhimmin mataki ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun takaddama tsakanin sassan biyu dangane da batun kasuwanci. Herman Van Rompuy, shugaban hukumar zartarwar tarayyar Turai ya ambata cewar, sassan biyu sun sami ci gaba mai ma'ana sakamakon tattaunawar da suka fara yi a wannan Alhamis, ta hanyar kaddamar da yarjejeniyar da ta shafi harkokin zuba jari, wadda ta hadar da bada kariya ga zuba jarin, da kuma bada damar shiga cikin kasuwanni. Herman Van Rompuy, ya fadi bayan muhimmin taron na wannan Alhamis cewar, China da EU sun yi amannar cewar, yanzu lokaci ya yi da ya kamata su tinkara gaba. Dama dai China ce kasa ta biyu mafi karfin tattalin arzikin a duniya, kuma dangantaka a tsakaninta ta Turai, ko da shike wani lokacin na fuskantar matsaloli, amma tana da muhimmanci ga harkokin cinikayya a duniya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman