Huldar cinikayya tsakanin Jamus da Indiya
December 12, 2010Shugabannin kasashen Jamus da Indiya sun yi alkawarin rubanya harkokin cinikayya a tsakaninsu nan da shekaru biyu masu zuwa. Hakan ya biyo bayan tattaunawar da ta gudana ce tsakanin Firaministan Indiya Manmohan Singh da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin. Shugabar gwamnatin ta Jamus ta shaidawa yan jarida cewa kasashen biyu za su kara yawan cinikayyar zuwa sama da euro miliyan dubu Ashirin kafin karshen shekarar 2012. A nasa bangaren Firaministan Indiya Manmohan Singh ya yaba da kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Indiya da Jamus. Shugabanin biyu sun yi ganawar ce a ranar Asabar din nan bayan taron da ya gudana tsakanin Indiya da kungiyar tarayyar Turai a Brussels inda suka cimma yarjejeniya ta fadada cinikayya ba tare da shamaki ba a tsakanin kungiyar tarayyar turan da Indiya.
Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala
Edita : Umaru Aliyu