1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Huldar Masar da Turkiyya

Usman Shehu Usman
September 4, 2024

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi yana ziyara a kasar Turkiya inda shuagaban kasar ta ya sauka a birnin Ankara da safiyar yau kuma ya samu gagarumar tarba daga Recep Tayyip Erdogan shugaban Turkiyya.

Türkei |  Treffen ägyptischer Präsident Abdel Fattah al-Sisi mit  Recep Tayyip Erdogan in Ankara
Hoto: Murad Sezer/REUTERS

Kasashen Masar da Turkiyya dai su ne kusan suka fi karfin fada a ji a siyasar Gabas ta Tsakiya musamman rikicin Palasdinawa da Isra'ila. Masu lura da siyasar kasashen biyu suka ce akwai matukar inganta hulda tsakanin Turkiyya da Masar a baya-bayannan, inda wasu ke cewa ziyarar Al-Sisi ya zo Turkiyya ne kawai don kara tabbatar da dinke wannan kawancen da kasashen biyu suka riga suka cimma. An dai dauki sama da shekaru goma da raba gari tsakanin kasashen biyu, har sai a watan Febrairun bana da shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Alkahira, wanda a nan ne shugabannin biyu suka ce sun shafi matsayinsu na baya kuma an bude sabon babi na hulda tsakanin kasashen biyu. Turkiyya dai ta kasance kasar da jami'an kungiyar Mulism Brotherhood ke fakewa, kungiyar da ta yi mummunar adawa da gwamnatin Al-Sisi bayan da ya kifar da gwamnatin Mohammed Mursi.