Faransa: Akwai sauran alaka da kasar Chadi
December 2, 2024Tun da farko ministan harkokin wajen kasar Chadin Abderaman Koulamallah ne ya bayyana sanarwar katse huldar sojan tsakanin kasashen, sai dai kuma ya jaddada kasashen biyu za su ci gaba da hulda a sauran fannonin rayuwa. Hakan dai na nuna cewa kasar ta Chadi ba za ta bi sahun kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar ba, wajen katse huldar diflomasiyya da uwar gijiyar tasu Faransa. Shi ma Shugaba Mahamat Idriss Déby na kasar ta Chadi ya ce matakin ba zai shafi hadin kai tsakanin kasashen biyu ba, yana mai cewa kasarsa za ta mayar da hankali kan wasu fannoni masu muhimmanci na dangantaka tsakaninta da Faransan. Yanzu da wannan matakin Faransa tana da sansanonin soja a kasashen Cote d'Ivoire da Senegal da Gabon, wadanda suka rage da sojojinta a tsofaffin kasashen da ta yi wa mulkin mallaka na nahiyar Afirka.
Kuma matakin na Chadi ya biyo bayan shirin kasar Senegal da ita ma ta ce za ta bukaci janye dakarun Faransa daga kasarta, abin da masana ke gani a matsayin gazawa na tsarin manufofin Faransa a nahiyar Afirka. A shekara ta 2013 wani rahoton kwamitin majalisar dattawan Faransa ya nuna cewa kaso 70 cikin 100 na kudin ayyukan soja a wajen Faransa ana kashe su ne a nahiyar Afirka, inda ake da rabin sojojin Faransa da suke kasashen ketere. Sannan irin wannan rahoto na shekara ta 2008 game da tsaron Faransan, ya nuna irin manufofin da suka dace wajen mayar da hankali a nahiyar musamman a kasashen Djibouti da Gabon da kuma Chadi. Rage yawan dakaru a kasashen ketere ba sabon abu ba ne, amma wannan karon Faransa tana fuskantar wani wadi na tsaka-mai-wuya game da kasancewar dakarunta a kasashen da ta yi wa mulkin mallaka a Afirka. Shugaba Emmanuel Macron na Faransan, na ci gaba da neman hanyoyin karfafa matsayin kasar a nahiyar Afirka.