1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Human Rights Watch ta wallafa sabon rahoto

April 27, 2021

A wani rahotonta da ta wallafa a wannan Talatar, kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta zargi Isra'ila da nuna wariya tare da bambanci kan Palasdinawa da larabawan da ke yankin.

Israel | Proteste | Zusammenstöß zwischen Juden und Palästinensern
Hoto: Hazem Bader/AFP

Zargin da Isra'ilar ta musanta. Kungiyar ta Human Rights Watch ta bukaci kotun hukunta masu aikata manyan laifuffuka ta ICC, da ta bude sabon bincike kan lamarin. Mahukuntan na Palasdinawa sun yi marhabin da wannan rahoton, inda suka yi fatan duniya za ta yi wani hubbasa dagane da batun.

Daraktan kungiyar na yankin yahudawa da Palasdinawa Omar Shakir ya ce sun jima suna jan kunnen hukumomin Isra'ila kan abinda ke faruwa na nuna wariya, amma suka yi kunnen uwar shegu. Nuna wariyar launin fata da ya samo asali daga kasar Afirka ta Kudu, ba wai ya tsaya kan bakar fata ba kawai, lamari ne da a halin yanzu ka iya shafar kowa da kowa.