1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceSiriya

Siriya: Ko zargin Isra'ila zai kawo sauyi?

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 17, 2025

Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta zargi Isra'ila da tilasta al'ummar kudancin Siriya barin gidajensu, bayan da Tel Aviv din ta bukaci a kwance musu damara.

Siriya | Shugaban Kasa Ahmad al-Shara  | Alaka | Isra'ila | Zargi | Human Rights Watch
Shugaban kasar Siriya na rikon kwarya Ahmad al-SharaHoto: Syrian Arab News Agency/APAimages/IMAGO

Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Human Rights Watch dai ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce sojojin Isra'la da suka mamaye kudancin Siriya tun watan Disambar bara sun gudanar da ayyukan cin-zarafi a kan mazauna yankin. 

Dakarun ISra'ila na ci gaba da kutsa kai SiriyaHoto: Israel Defense Forces/Anadolu Agency/IMAGO

Matakin na Isra'ila dai, na zama wani bangare na kokarin da sabuwar gwamnatin Siriya ke yi na cimma yarjejeniyar tsaro da makwabciyar tata. A cewar kungiya, tilasta al'ummar yankin ficewa daga gidajensu, aikata laifukan yaki ne.

Wannan na zuwa ne bayan da kafafen yada labaran Siriyan suka bayyana cewa, sojojin Isra'ilan sun cafke mutane da dama a kudancin kasar kwana guda bayan da Damascus din ta ce tana aiki tare da Washington domin cimma matsaya guda ta tsaro da Isra'ilan.