1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hungary: Matsaya kan shigar Sweden kungiyar NATO

February 26, 2024

Ana sa ran majalisar dokokin Hungary ta cimma matsaya kan kasar Sweden na son shiga kungiyar kawancewan tsaro ta NATO.

Firanministan Sweden, Ulf Kristersson da takwaransa na Hungary, Viktor Orban
Firanministan Sweden, Ulf Kristersson da takwaransa na Hungary, Viktor OrbanHoto: Denes Erdos/AP Photo/picture alliance

Ana sa ran 'yan majalisar za su kada zaben amincewa da bukatar Sweden din na zama mamba a kungiyar a NATO, ko da yake tuni kwamittocin majalisar suka amincewa da hakan.

Dama dai Hungary ce kasa ta karshe cikin kasashen mambobin kungiyar 31 a kungiyar ba ta amincewa Sweden din ba. Tun dai a watan Mayun shekarar 2022 ne dai kasar Sweden ta nemi shiga kungiyar ta NATO, sai dai ta fuskanci jinkirin amincewar kasashen Turkiyya da Hungary. A farkon watan Afrilun bara ce, aka amince da kasar Finland a matsayin mamba ta 31 a kungiyar.