1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

130109 Jugendherbergen

August 27, 2009

An cika shekaru 100 da Richard Schirmann ya ƙirƙiro husa´ar kafa wuraren hutawar matasa masu kama da ƙananan hotel wato "Youth Hostel"

Ɗaki a wani ƙaramin hotel na matasa wato "Youth Hostel"Hoto: Långholmen's Youth Hostel

26 ga watan Ogusta na shekara ta 2009,kwana ta shi, an cika shekaru 100 daidai, da ƙirƙiro husa´ar nan ta kafa wuraren shaƙatawa na yara matasa a nan ƙasar Jamus, wadda ta bazu a sauran ƙasashen duniya, ta kuma rikiɗa zuwa wani dandalin cuɗe ni in cuɗe ka tsakanin matasa daga ko wane ɓangare.

Richard Schirmann na ƙasar Jamus, malamamin makaranta ne da ya fara tunanin ƙirƙiro husa´a girka ɗakunan hutawa na matasa ,hasali ma dai ´yan makaranta a lokatan hutu, kokuma yawan shaƙatawa.

Komi dai shina da dalili,Richard Schirmann,ya samu wannan tunani, bayan azabar da suka sha tare da ´yan makararsa, a yayin wani yawan buɗe ido, inda ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya rutsa da su , sannan suka sami kansu a cikin halin rashin wurin kwanciya kyakkyawa.

Shekaru ukku bayan farakon wannan tunani ,ya girka gidan hotel ɗin matasa na farko a garin Altena dake yankin Nordrhein Westlafiya na ƙasar Jamus, a cikin harabar makarantarsa. A shekarar ta farko, an girka wuraren saukar matasa baƙi har 140, ta la´akari da karɓuwar da husa´ar ta samu daga jama´a.

Sannu a hankali wannan ƙananan Hotel suka cigaba da bunƙasa, inda a tsukin shekaru biyar yawan su ya tashi 500.

A farkon shekarun 1920, ƙasashe maƙwabtan Jamus da sauran ƙasashenTurai, kamar su Poland,Holland, Faransa,Suizland, da Engla suka fara kwaikwayan husa´ar ta ƙasar Jamus.

Ƙiddidiga ta nunar da cewar, kawo yanzu, akwai irin wannan wurare a ƙalla dubu biyar,a duniya, inda mutane fiye da miliyon goma ke amfani da su ako wace shekara.

To saidai a cewar Thorsten Richter mai kula da wuraren karɓar matasan na yankin arewa maso yammacin Jamus, a halin da ake ciki wannan gidaje sun fara raguwa matuƙa.

"A Bremen alal misali, muna da wani gida wanda a yanzu muka rufe, muka kuma saida, muka zuba ƙarin jarin kuɗin a cikin gidajen dake da saura yanzu."

A tsukin shekaru takwas da suka wuce tsakanin Ostfriesland, zuwa Osnabrück a nan Jamus,an rufe wuraren shaƙatawa na matasa 15, wato kimanin kashi ɗaya cikin ukku, na jimlar wuraren, sannan wanda ke da saura basu da tasiri kamar na baya.

Saidai kuma, an samu cigaba ta wani ɓangaren domin ba matasa kaɗai ke amfani da wuraren ba.

Magidanci zai iya ɗaukar iyalansa ya kai su, saboda farashi mai sauƙi, kamar yadda Richter ya nunar:

"Wani shugaban asibiti ya zo nan a abaya tare da iyalan.Sun saba zuwa hutu a tsibirin Mauritus cikin baban hotel amma yace daga yanzu, a duk shekara zai kawo yaransa aƙalla so guda anan , domin su shaƙu da saura, su ga kuma yadda tsarin rayuwa yake."

A tunaninsa na farko, Richard Schrimann, ya ya gano cewar, wannan mataki zai baiwa matasa jamusawa damar sanin lunguna dabamdaban na ƙasa, sannan su shaƙu da sauran dangi matasa daga Jamus ko daga wasu ƙasashen duniya.

Wani baban cigaban da aka samu a cikin wannan husa´a ta girka ɗakunan matasa shine, girka Ƙungiyar ƙasa da ƙasa wadda ta ƙunshi dukkan ƙanana Hotel masu ɗauke da burin cuɗe in cuɗe ka tsakanin matasa daga dabamdabam,na duniya ba tare da bambancin addini , launin fata ko jinsi ba.

Mawallafi:Schellhass,Jens/ Yahouza

Edita:Awal