1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Husni Mubarak na fama a Asibiti

June 20, 2012

Tsohon shugaban Masar, Husni Mubarak na cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai bayan da ya kamu da hawan jini

epa02680277 (FILE) A file picture dated 18 August 2009, shows the then Egyptian president Hosni Mubarak looking on during his meeting with President Barack Obama in the Oval Office of the White House in Washington D.C., USA. The El Arabiya TV channel on 10 April released an audio speech from the Former Egyptian President recorded in Sharm el Sheikh in Egypt the 09 April. During his speech, Mubarak denied that he has any assets outside the country, it is the first public comments he has made since his ouster, he also said that he would agree to any measures taken to reveal any bank assets or real estate he owns abroad. Mubarak stepped down on February 11 after an 18 day uprising across the country. EPA/DENNIS BRACK/POOL
Hosni MubarakHoto: picture-alliance/dpa

Kafafen yada labaru masu zaman kansu a kasar Masar sun ba da rahotannin da ke nuni da cewa tsohon shugaban kasar, Husni Mubarak na cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai bayan da ya kamu da ciwon zuciya. Tun da farko kamfanin dillacin labarun gwamnatin kasar wato MENA ya sanar da mutuwar tsohon shugaban. To ama sai majalisar koli ta sojin kasar ta karyata hakan. A jiya talata ne dai ake dauki Mubarak zuwa wani asibitin soji bayan da ya kamu da ciwon hawan jini.

A farkon shekarar 2011 ne Mubarak ya yi murabus daga matsayinsa na shugaban kasar bayan da jama'a suka shafe makonni suna gudanar da zanga -angar nuna adawa da gwamnatinsa. Shi dai tsohon shugaban da ya shafe shekaru kusan 30 yana jan ragamar kasar a farkon watan Yuni kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa laifin kashe mutane sama da dari 800 da suka shiga zanga-zanga nuna adawa da shi a shekarar 2011 .

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu