ICC: Bukatar kama shugaban mulkin sojin Myanmar
November 27, 2024Talla
Babban mai gabatar da kara na kotun shari'ar manyan laifuka ta duniya ICC Karim Khan a yau Laraba ya bukaci alkalan kotun su bayar da sammacin kama shugaban gwamnatin mulkin sojin Myanmar bisa laifukan da aka aikata kan musulmi yan kabilar Rohingya marasa rinjaye.
Gen. Min Aung Hlaing wanda ya kwace mulki daga shugabar da aka zaba ta dimukuradiyya Aung San Suu Kyi a juyin mulkin 2021 an zarge shi da laifukan cin zarafin al'umma da azabtarwa da kuma korar yan kabilar Rohingya daga kasar.
Mutane kusan miliyan daya aka tilasta wa yin kaura zuwa kasar Bangladesh mai makwabtaka domin tsira da rayukansu, lamarin da ake gani kokari ne na kakkabe kabilar da yi musu fyade da kisa da kuma kone gidajensu.