ICC ta gano shirin yi mata zagon kasa
October 2, 2013Kotun hukunta laifukan yaki ta ICC da ke birnin Hague na kasar Holland ta bada sammacin kamo wani mutum da ta ce tana zargi da yin kafar ungulu ga shari'ar da ake wa mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto kan rikicin bayan zaben shugaban kasar na 2007 da yai sanadiyyar rasuwar mutane da dama.
Mai shari'a Cuno Tarfusser ne ya ambata hakan a wannan Larabar, lokacin da ake cigaba da sauraron shari'ar ta Mr. Ruto, inda ya ce kotun ta bankado shirin da mutumin mai suna Walter Basara ke yi na bada cin hanci ga wani mutum da zai bada shaida gaban kotun.
Ita ma dai babbar mai gabatar da kara ta kotun Fatou Bensouda ta ce ta fara gudanar da bincike kan wasu gungun mutane da ke kokarin dagula lamura a shari'ar da ake musamman ma dai yin katsaladan ga irin bayanan da masu bada shaida za su yi a gaban kotun.
Kawo yanzu dai mutumin da ake zairgi bai ce uffan ba amma idan dai kotun ta tabbatar da zargin da ake masa to zai fuskaci daurin shekaru biyar ne a gidan maza.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita. Umaru Aliyu