1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ICC ta samu jagoran yan tawayen Uganda Kony da laifukan yaki

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 6, 2025

Daga cikin laifuka 39 da Joseph Kony ya aikata akwai kisa da yi wa mata fyade da tilasta shigar da kananan yara soja.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC
Hoto: Nicolas Economou/NurPhoto/picture alliance

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta tabbatar wa jagoran 'yan tawayen kungiyar LRA ta Uganda Joseph Kony da aikata laifukan yaki da cin zarafin jama'a, wadanda ya aikata daga shekarar 2002 zuwa 2005.

Daga cikin laifuka 39 da Joseph Kony na Lord's Resistance Army ya aikata a wadannan shekaru, sun hada da kisa da yi wa mata fyade da tilasta shigar da kananan yara aikin soja da dai sauran nau'ikan azabtar da bil'adama.

Karin bayani:Ficewar kasashen AES daga kotun ICC

Tun a shekarar 2005 kotun ta ICC ta bada umarnin kamo shi a duk inda ya ke, kuma har yanzu ake ci gaba da nemansa, kasancewar kotun ta tabbatar da samunsa da aikata laifukan ba tare da halartarsa zamanta ba.