1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun ICC ta wanke Laurent Gbagbo

Ramatu Garba Baba
March 31, 2021

Kotun ICC ta wanke Laurent Gbagbo daga zargin laifukan yaki da aka tafka bayan zaben shugaban kasar Ivory Coast inda dubbai suka rasa rayukansu.

Niederlande Den Haag I Prozess Elfenbeinküste am Internationalen Gerichtshof
Hoto: Jerry Lampen/AP/picture alliance

Bayan kwashe shekaru goma ana shari'a, a wannan Laraba, kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ta wanke tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo, daga duk wasu zarge-zargen da ake masa na aikata laifukan yaki a rikicin bayan zaben da ya sha kayi a shekarar 2010. Tun dai a shekarar 2011 aka mika shi a gaban Kotun ICC da ke birnin Hague, don hannu a tashe-tashen hankulan da rayuka fiye da dubu uku suka salwanta, baya ga jefa kasar cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali.

Kotu ta yanke hukuncin ne bayan da ta ce masu shigar da kara sun gagara gabatar da kwararan hujjoji da za su tabbatar da ya aikata laifukan. Laurent Gbagbo, ya kasance tsohon shugaban wata kasa a duniya, da aka soma gudanar da shari'arsa a karon farko a gaban kotun na ICC. Baya ga shi kotun ta wanke Charles Ble Goude, wanda shi ma ake tuhumarsu tare da shi a shari'ar.