1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC za ta dakatar da bincike kan Dafur

Ahmed SalisuDecember 13, 2014

Kotun ICC da ke hukunta laifukan yaki ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa za ta dakatar da bincike kan zargin aikata laifukan yaki a yankin Dafur.

Bosco Ntaganda Prozess ICC Den Haag 10.01.2014 Bensouda
Hoto: Reuters

Fatou Bensouda da ke zaman babbar mai gabatar da kara a kotun ta ICC ta ce wannan mataki da suka dauka ya zama wajibi domin kuwa ya zuwa yanzu babu wanda aka hukunta kana kwamitin na sulhu bai taka wata rawar gani ba wajen taimakawa don kawo karshen laifukan yakin da aka tafka a yankin.

Rikicin yankin Dafur dai na daga cikin batutuwan da aka gabatar gaban kotun ta ICC sakamakon zub da jinin da aka yi cikin shekara ta 2003 lokacin da 'yan tawaye suka yi fito na fito da mahukuntan gwamnatin Sudan wadda Shugaba Omar al-Bashir ke jagoranta.